YADDA AKE KOSAN BUREDI DA KWAI

KOSAN BUREDI DA KWAI

*********************
Abubuwan da ake bukata:
• Garin biredi
• kwai
• Attarugu
• Magi
• Kori
• Garin tafarnuwa
HAdI
******
A samu biredi sannan a guggutsura shi kanana har sai ya bushe sannan a mutsuttsuka shi da hannu a saui garin. Ko kuma za a iya sayan garin biredi a manyan shagunan da ke sayar da kayan abincin zamani. A fasa kwai kamar biyar a ciki sannan a zuba magi. A jajjaga attarugu da tafarnuwa a zuba da kori. Sannan a kwaba sosai.
A samu tukunyar tuya a dora a kan wuta a zuba man gyada da albasa. Bayan ya yi zafi sai a sa cokali a rika gutsura kullun kamar yadda ake gutsura kullun kosan wake ana zubawa a cikin man gyadan. Idan dayan gefen ya soyu sannan a sake juyawa zuwa dayan gefen domin ya soyu. sannan a sauke.
Za a iya cin wannan irin kosan da kunu ko kuma shayi da safe ko a duk lokacin da ake bukata. A ci dadi lafiya

Comments