YADDA AKE HADA FATEN DOYA

FATEN DOYA
INGREDIENTS:
1.Yam
2.Meat
3.Carrots, green beans,peas
4. Albasa, tattasai, tarugu, tafarnuwa
5. Oil, ko manja
6. Seasonings and spices.
PROCEDURE: Ki sami doya kiyi per boiling nashi, ki sauke ki fitar da ruwan nan mai kauri ki ajiye a sieve, ki tafasa namanki da albasa da gishiri, idan ya dahu sai ki tsame naman, ki sa mai a wuta ki soya shi, amma sama sama, idan ya huce sai ki yanka shi kanana sai ki mayar dashi cikin ruwan naman kafin ki gama haďa sauran.
Daga nan sai ki jajjaga kayan miyan ki duka, ki yayyanka carrots da green beans. Farko ki sa tukunya a wuta, sai ki zuba manja ko mai, sai ki dauko kayan miyan ki zuba a ciki, ki dan soya shi. Sai a ďauko ruwa dan dai-dai a zuba, ki sa maggi, gishiri, curry da thyme dss, ki dauko naman da ruwan naman ki juye, sai ki jujjuya komai ya hadu, sai ki dauko doyan ki juye ciki, idan ya kusa karasawa sai ki zuba carrots da green beans da peas ki rufe, bayan kamar 5 to 8mnt sai ki duba ki sauke.
Note: Sai an kula da ruwan da za a sawa doyan, doya bata son ruwa sosai, don haka ruwa dan kadan zaki sa mata ya isheta. Sannan zaki ga ruwan faten doyan ba yi da kauri shi haka ake yinsa. Sannan wurin maggi da gishiri a kula, Bcs ruwan namanki akwai maggi da gishiri. Sannan zaki iya sa crayfish.
ko Kuma
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake faten doya. Faten doya dai girki ne wanda kowa ya san shi. Wani hanzari ba gudu ba, yadda wata za ta girka na ta daban da yadda wata matar za ta girka na ta faten doyar. Wata idan ta yi wannan girkin sai a ga doya daban da ruwa da manja ko kauri fatan bai yi ba. Sai a ga Manyan gobe ba su sha’awar cin abincin. Dole ne mata su dage da girka nau’ukan girke-girke yadda manyan gobe za su rage yin kwadayi idan an je unguwa.
Abubuwan da ake bukata
  1. •Doya
  2. • Manja
  3. • Alayyahu
  4. • Dakakken ‘cray fish’
  5. •Albasa
  6. • Attarugu
  7. • Timatir
  8. • Bandan kifi
  9. • Nama
  10. • Tafarnuwa
  11. • Citta
  12. • Magi
  13. • Kori
Hadi
A samu Doya danya a fere, a yayyanka kanana sannan a wanke a ajiye a gefe. Bayan haka sai a samu ganyen alayyahu shi ma a yayyanka amma manya-manya a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe. A sulala nama da albasa da gishiri kadan sannan a sauke.
A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja sannan a zuba albasa da tafarnuwa da garin citta da yankakken attarugu da timatir. A yi ta gaurayawa har sai sun soyu. Sannan a zuba ruwan nama da naman da magi da kori a wanke bandan kifi a zuba da ‘cray fish’. Idan ya dan tafasa sai a dauko wannan doyar a zuba a ciki. Idan ta yi laushi sai a samu muciyar tuwo a dan faffasa doyar sama-sama yadda ruwan zai yi kauri sannan a dauko yankakken alayyahu a zuba na tsawon minti biyu zuwa uku. Idan ya nuna sai a gauraya a sauke. A ci dadi lafiya.

Comments