YANDA AKE HADA WAINA TA ZAMANI

Yadda a ke Masa
Abubuwan hadawa
  • Shinkafa ta tuwo  kofi 2
  • Yeast chokali 2
  • Baking hoda chokali 1
  • Dafaffen shinkafa(ya dahu sosai) 1/3 kofi
  • Sugar
  • Albasa 1
  • Attarugu 3
  • Mai
Yanda ake hadawa
  1. Da farko dai za ki wanke shinkafarki,ki jikata da safe, da yamma a kai markade.
  2. Idan a ka kawo, sai ki juya ki zuba yeast da sugar da baking hoda, ki juya sosai, sai ki rufe, kisa awaje mai dumi.
  3. Da safe ki yanka albasa kanana a kai, sannan ki jajjaga attarugu ki zuba, ki sa dafaffen shinkafarki, ki juya, ki sa ruwa dan daidai yayi kauri amma ba sosai ba.
  4. Sai ki dauko kaskon tuyar masa kisa mai yayi zafi, sai ki rika zuba kullinki kadan-kadan, idan kasan yayi sai ki juya daya gefen, idan ya soyu ki kwashe, haka za ki tayi har ki gama.
  5. Masa a na cinta da miyar taushe ko ganda.
Na gode, sai mun hadu a gaba
WAINAR SHINKAFA
1. Shinkafa tuwo Mudu/loka daya
2. Shinkafar dafawa gwangwani biyu
3. Yeast tea spoon daya
4. Oil, albasa da kanwa.
PROCEDURE: Farko za a sheqe shinkafar tuwo, a dauraye sannan a jiqa yayi awa biyu zuwa uku, sannan a sake wankewa a kai niqa, sai a dafa shinkafar ci a zuba a kai. A yanka albasa isashe a ciki sai a kai injin niqa. Niqa mai kauri za a miki kada a sa ruwa ko kuma ki tabbata ba a lafta ba. Bayan an amso sai a jujjuya a zuba yeast a sanya shi a rana ko wurin dumi yanda zai tashi. Idan kuma gobe ne zaki yi kamar da safe ko da rana to zaki iya barin sa ya kwana qullun yanda zai tashi da kyau.
Washe gari sai a jujjuya, zaki iya niqa albasa ki zuba a kwano daban, ki sake samun kwano da zaki rinqa diban qullun, ki dandana in akwai tsami ki zuba ruwan kanwa, sai ki debi niqaqqen albasa kadan ki zuba, ki saka sugar kadan in kina so, ko ki jujjuya su sannan in tanda ya fara zafi a fara suya, kuma a kula sosai a tabbata wuta bayyi yawa ba, sannan idan manya kike yi to ki dan samu tsinken da zaki rinka sokawa a ciki don ki tabbatar cikin ya nuna kafin ki kwashe. Zaki iya yi a tandar qarfe a risho.
Note: Wasu basu zuba albasa lokacin niqa sai in za a soya kamar yanda na fadi, wasu kuma suna saka duka, a niqa da lokacin suya. Kuma wasu da baking powder suke kashe tsamin ba kanwa ba.Wannan shine simple way na yin waina.
SINASIR
Duka kwabin waina da sinasir ďaya ne, iyaka dai sinasir yafi sauqi, babu hayaki babu komai, shi zaki samu frying pan ne ki sa mai kamar table spoon sai ki zuba qullu daga nan ki rufe, ki sa wuta kadan kadan, a hankali zaki ga qullun yana tsotsewa har ya zama fari babu kullum a sama sai ki cire. Ba a juya sinasir haka ake yin sa.
Note: Yana da kyau ki samu non stick frying pan saboda gujema kamawa, sannan in sun sha iska zaki iya hada bibbiyu kina sakawa a cikin ledan santana.

Comments