YADDA AKE HADA MIYAR KABEJI DA NAMA

Miyar kabeji da nama
yadda ake miyar kabeji mai nama. Wannan irin miya tana kara lafiya a jiki sannan tana da dadi idan aka hada ta da farar shinkafa ko da dafaffiyar doya da kuma farar taliya da sauransu. Yana da kyau uwargida ta koyi yadda za ta rika canza dandanon miyarta a koda yaushe. Samun canji a dandanon girki na da alaka da irin kalar magi da kuma kayan kanshin da ake sa wa a lokacin girkin.
Abubuwan da za a bukata 
• Kabeji
• Nama
• Man gyada
• Attarugu
• Albasa
• Tumatir
• Magi
• Kori
• Tafarnuwa
Hadi:
Da farko za a samu kabeji sannan a yayyanka  manya-manya sannan a wanke da ruwan gishiri domin kashe kowace irin kwayar cuta da ke ciki sannan a yayyanka albasa da tumatir kwaya biyu kacal sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa.
Daga nan sai  wanke nama sannan a silala da albasa da gishiri kadan bayan ta yi laushi, sai a yayyanka kanana sannan a soya sama-sama. Bayan haka, a dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da tumatir da kuma jajjagen attarugu da tafarnuwa a soya. Sannan a dauko naman a zuba ba tare da romon ba. A zuba magi da kori a gauraya a jira su tafasa sau daya sannan a zuba kabejin a gauraya a dan rufe. Bayan mintuna biyu, sai a sake budewa a gauraya sannan a rufe na tsawon mintuna uku sannan a sauke.
A dora a kan shinkafa dafa-duka zazzafa ko kuma farar shinkafa da makamancinsu. A ci dadi lafiya!

MORINGA SALAD (KWADON ZOGALE
INGREDIENTS:
  • 1. Tafasashen zogale
  • 2. Quli-Quli
  • 3. Cucumber, tumatir da albasa
  • 4. Garin yaji 
  • 5. Sugar in kina so.
  • 6. Maggi and gishiri.
PROCEDURE: Ki daka Quli amma ki zuba maggi da gishiri yanda zai fito sosai. Sai a yanka tomatoes masu kyau qanana, a yanka albasa shima 'yan manya kaďan. Sai a yanka cucumber yan madaidaita a ciki.
Daga nan sai ki juye su a cikin zogalen, ki zuba quli yanda zai ji, ki zuba yaji yanda kike so sai a motsa ya hade sosai. Idan kina so da sugar iri na sai ki zuba yanda kike so. Habawa! In maigidanki mai son zogale ne kika masa wannan in shaa Allahu zai yaba. Sannan in kina son yayi danqo zaki iya ďiga masa ruwa kaďan. Nayi jiya amma tsakani na da zogale akwai amana na cinye na manta in ďauki picture
Kun san dai amfanin sa dayawa ko especially mu mata yana gyara mana jiki da kashe infection da saukar da ni'ima. Wasu suna zuba lemun tsami, carrots, tattasai ko tarugu, green pepper, hanta da sauran su. Amma ni nafi son shi haka.
Ke ya kike yin naki zogalen? So nawa kike cin sa a wata? Kin san abun da kike rasawa kuwa in baki ci? Kina shan ruwan sa?

Comments