YADDA AKE HADA MIYAR HANTA

Abubuwan hadawa

  • Hanta rabin kilo
  • Attarugu 4
  • Tattasai 3
  • Albasa 2
  • Maggi 5
  • Gishiri
  • Citta 3
  • Tafarnuwa 2
  • Kori (Curry)
  • Onga
  • Man girki

Yanda ake hadawa

  1. Da farko dai uwargida zaki wanke hantar kiyanka daidai misali
  2. Saiki sa a tukunyarki ki yanka albasa, kuma ki sanya maggi kwaya daya da dan gishiri
  3. Idan yayi sai ki sauke ki kwashe a wani kwano, sai ki zuba mai da kayan miyanki ki soya ya soyu da kyau
  4. Idan ya soyu sai ki zuba ruwa kadan ki sa hantar ki kawo maggi, da gishiri, da citta, da tafarnuwa, da kori ki sanya
  5. Sai ki barshi kamar minti shabiyar zaki ji gida yadau kamshi sai ki sauke
Ita dai wannan miyar zaki iya cinta da shinkafa ko tuwon sakwara. A ci dadi lafiya.

Comments