YADDA AKE HADA KOSAN DOYA

KOSAN DOYA
KAYAN HADI
  • Doya
  • Kwai
  • Nama
  • Fulawa 
  • Albasa 
  • Attarugu
  • Gishiri 
  • Maggi

*YADDA ZA'A HADA*
Ki fere doya ki dafa ta sai ki daka sama sama ko kuma ki murmushe sannan ki samu albasa da attarugu ki jajjaga ki hada da doyarki da kika daka ki sa maggi da gishiri, ki tafasa nama ki jajjaga a turmi ki kwashe ki zuba a ciki ki juya sosai sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai sai ki jefa a fulawa ki saka a cikin man gyada mai zafi ki soya shi, idan yayi brown sai ki kwashe daga cikin man gyadan,,wannan girke kam ba za'a bawa yaro mai 'kiwiya ba
Yadda ake Samosa
Abubuwan hadawa
  • Fulawa (flour)
  • Kwai
  • Nama
  • Maggi
  • Onga
  • Kori (Curry)
  • Gishiri
  • Man gyada
  • Attarugu
  • Albasa
  • Karas (carrot)
  • Baking powder
Yadda ake hadawa
  1. Da farko zaki wanke namanki ki tafasa shi da albasa da maggi da gishiri da dan korinki. Ki yi shi tamkar danbun nama.
  2. Sai ki goga karas din ki, ki kuma soya shi
  3. Sai ki zuba fulawarki a roba ki saka baking powder da dan gishiri ki kwaba. Ki murza ta murzu sosai ta yi fadi.
  4. Sai ki rika yankawa kina zuba namanki da karas kina nadewa kamar dan kwali
  5. Sai ki dora mangyadarki a wuta ya yi zafi
  6. Idan yayi zafi sai ki dinga jefa nadadden samosanki kina kisoyashi
Fanke
Abubuwan hadawa
  • Fulawa
  • Sugar
  • Yeast
  • Mai
 Yanda ake hadawa
  1. Da farko uwargida za ki tankade fulawarki a roba mai kyau mai murfi.
  2. Sai ki zuba yeast da sugar da ruwa ki kwaba ya kwabu sosai(ya yi ruwa-ruwa in da zai rika kamun hanu) sai ki rufe  a wuri mai dumi.
  3. Ya sami kamar awa 1 ko 2 , idan ya yi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mai ya yi zafi.
  4. Anan sai ki rinka deban kullin da ludayi kina sawa a cikin mai kina soyawa ya yi jan suya. Ana iya ci da shayi ko wani lemo
Sai mun hadu a girki na gaba. Na gode

Comments