YADDA AKE HADA FARFESUN DANKALI

Farfesun Dankali
Yadda ake girka farfesun dankalin turawa da kaza wanda aka fi sani a turance da ‘potatoe peper soup’. Domin sanya kunnen maigida motsi, yakamata a rika dagewa wajen koyon girkin zamani. Girki dai shi ne sirrin zaman aure sannan iya girka abinci daban-daban na sanya maigida da yara cikin farin ciki da annashuwa inda za su rika rububin komawa gida da wuri.
Abubuwan da za a bukata:
  • · Kaza
  • · Dankalin turawa
  • ·   Kori
  • ·  ‘Thyme’
  • · Karas
  • ·  Attarugu
  • ·   Tumatir
  • ·  Gishiri da magi

Hadi:
Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta yanka shi kanana, daga nan sai ka wanke zazanta. Ka fara tafasa kazar da attarugu da kori da garin tafarnuwa da citta nda magi da tumatir da ‘thyme’. Idan ya dan dahu, sai ki zuba yankakken dankalin turawar a ciki da koren wake da kuma yankakken karas.   Uwargida na iya yin irin wannan girki da safe don a karya.
Ina son janyo hankalin masu karatu cewa duk macen da take zuba man gyada a farfesu to da sauranta a girki, saboda farfesun kaza ko na kifi ko na nama da dai sauransu na dauke ne da kitsen ya wadatar.

Faten Dankali (Irish Potato)
Abubuwan hadawa
  • Dankali
  • Attarugu
  • Albasa 
  • Maggi
  • Cittah
  • Kifi  (ice fish).
  • Alayyahu
  • Kori
  • Man gyada
Yanda ake hadawa
  1.  Da farko uwar gida zaki fere dankalinki, ki yanka daidai misali.
  2.  Sai ki wanke kifinki, ki cire dattin, ki yanka gunduwa-gunduwa, ki zuba albasa da maggi da cittah a kai, sa'annan ki dora a wuta.
  3.  Bayan haka sai ki jajjaga attarugu da albasa da cittah ki ajiye.
  4.  Sai ki duba kifinki, idan ya tafasa ki sauke ki barshi ya dan huce, in ya huce sai ki bare shi ki ajiye.
  5.  Anan sai ki dauko tukunya, ki zuba manki ki yanka albasa a ciki, ki barshi ya soyu kadan.
  6.  Kisa jajageggen attarugu da kika jajjaga, sai ki zuba ruwa daidai misali, ki rufe yayi mintina ya tafasa.
  7.  Idan yayi sai ki zuba dankalinki, ki sa maggi da gishiri kadan da kori da cittah, ki rufe ya nuna.
  8.  In yayi sai ki zuba kifinki da alayyahu da albasa, ki juya, ki taba ki ji, idan komai yayi sai ki rufe, ki barshi yayi minti biyar.
  9. Shi ke nan, ki sauke, ki zubawa mai gida da yara, a ci dadi lafiya.
Na gode, sai mun hadu a girki na gaba.
Hadin Dankalin Turawa na musamman
Abubuwan hadawa
  • Dankali (Irish)
  • Kwai 5
  • Attarugu 4
  • Albasa 2
  • Maggi 4
  • Gishiri
  • Kori
  • Tafarnuwa
  • Koren tattasai 1
  • Mangyada
Yanda ake hadawa
  1. Da farko zaki fere dankalinki kiyanka ki zuba gishiri kadan sai ki rufe ki dora a wuta ki tafasa.
  2. Idan yayi sai ki sauke ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki ajiye agefe.
  3. Sannan sai ki kawo tukunya mai fadi kamar kasko sai ki zuba mangyada ki dora a wuta kisa dankalinki, sannan ki zuba kayan da kika jajjaga.
  4. Sai ki juya a hankali, ki fasa kwainki, ki zuba maggi da kori sai ki juya har yayi. Idan yayi sai ki sauke ki juye.
Na gode.

Comments