YADDA AKE HADA FANKASU

FANKASAU
1. Alkama rabin loka
2. Yeast tea spoon 1
3. Flour gwangwani 3
4. Mai
PROCEDURE: Farko zaki kai alkama a niqa miki sai ki tankade da rariyan laushi shima flour a tankade shi a ciki. Sai ki zuba ruwa kiyi ta juyawa har sai ya hade sosai. Kwabin kamar na fanke amma yafi fanke tauri sosai.
Sai ki rufe a barshi ya tashi sosai. Idan da daddare ne zaki soya da safe kina tashi kamar saura hour ďaya ki soya sai ki buga shi sosai da sosai. Idan kin ji akwai tsami zaki iya dan zuba ruwan kanwa ki buga. Sai ki rufe lokacin da zaki soya zaki ga ya sake tasowa sosai.
Sai a saka mai a wuta in yayi zafi sai a rinqa debo kwabin ayi fadi dashi ayi huji a tsakiya sannan a saka a mai ya soyu. In so samune a mata miyan ganye a zuba man shanu a kai shi zuwa bakin salati. Ga sauki ga dadi. Please don't mind my pictures ina da shan miya.
Note: Ana yin zallan kwabin da ruwan tsamiya amma ya kan sashi qarfi da tsami. Wani kuma zaki ga baya yi sai kaďan sai ki sa kanwa don ya kashe tsamin. Sannan koda baki cin fankasau kamar ni idan kina yin na flour nan tsaf zaki ci. Zaki iya jiqa yeast ďin da ruwan dumi musamman idan a ranar zaki yi. Fankasau akwai sauqi a yiwa maigida a canza baki. Ba a cika flour don zai sha miki mai kuma ba zayyi taushi ba. Idan na zallan alkama ne duka kwabin ďaya ne.

Comments