YADDA AKE HADA FATEN KUSKUS

FATEN KUSKUS
*ABUBUWAN BUKATA* 
  • Jakar Kuskus daya(1)
  • Man gyada ko Manja
  • Maggi 4 Ko Rayko (4)
  • Gishiri, Curry
  • Kayan Miya daidai Misali
  • Alayyahu Yadda kike so
  • Gyadar miya Gwangwanin tumatir
*YADDA AKE YI*
Zamu soya kayan miyan da muka jajjaga a manja ko mangyada sai mu zuba ruwa kwanon sha, sannan mu zuba su maggi da dakakkiyar gyadar miya da curry da gishiri, idan ruwan ya tafasa sai mu dauko kuskus mu dinga zubawa ahankali muna juyawa har mu gama. Sai mu rufe amma mu dinga yi muna juyawa don kada ya dunkule, idan ya nuna sai mu kawo yankakken Alayyahun da AlbaSA mu zuba idan suka nuna sai mu sauke.

Comments