YADDA AKE HADA DANBUM NAMA

Danbun Nama
Abubuwan hadawa
  • Nama mara kitse kilo
  • Attarugu
  • Maggi (6)
  • Albasa
  • Gishiri
  • Tafarnuwa
  • Cittah
  • Mangyada
  • Kori
Yanda ake hadawa
  • Da farko zaki wanke namanki ki sa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa ya nuna sosai.
  • Idan yayi sai ki sauke ki kawo turminki mai kyau ki daka namanki ya daku sai ki kwashe.
  • Sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki zuba akan dakekken namanki kisa, sannan ki sa maggi da kori ki juya sosai komai ya hadu.
  • Idan yayi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada ki zuba namanki ki yi ta juyawa har sai yayi yanda kike bukata.
  • Idan yayi sai ki sauke ki juye a wani abu mai kyau.
Na gode

Comments