YADDA AKE HADA DANBUM ACCA

Abubuwan hadawa 

  • Acca kofi biyu
  • Karas 2
  • Kabeji 1/6
  • Albasa 1
  • Attarugu 2
  • Mai cokali 2
  • Maggi
  • Gishiri
 

Yadda ake hadawa

  1. A wanke Acca sannan a rege a zuba a madambaci ya yayi rabin dahuwa.
  2. Sai a sauke a yanka kabeji, da karas, da albasa, da attarugu, sannan da alayyahu.
  3. Sai a cakuda gaba daya harda accar a zuba mai, da maggi sannan da gishiri.
  4. A nan sai a sake mayarwa kan wuta ya karasa dahuwa. Da ya dahu shi ke nan danbun acca ya kammala sai a sauke a rarraba a sawa kowa na shi.

Comments