YADDA AKE HADA DAN WAKE

Abubuwan hadawa
  • Shinkafar tuwo
  • Fulawa (flour)
  • Kuka
  • Kanwa
  • Man gyada
  • Maggi
  • Yaji
Yadda ake hadawa
  • Da farko zaki sami shinkafarki ta tuwo kiwanke ta fita tas
  • Sai ki kawo ruwan duminki mai zafi sosai ki zuba akan wankekken shinkafarki ya dan yi kamar minti 20
  • Bayan ya yi kamar minti 20, sai ki tsanyaye ruwan ki bayar a kai miki inji a markada. Kar a sa ruwa a yi shi da kauri
  • Bayan an markada sai ki kawo fulawarki ki tankade a kan markadadden shinkafarki, sai ki saka kuka da ruwan kanwar da kika jika
  • Sai ki kwaba sai yayi daidai kaurin da ki ke so
  • Sannan sai ki fara sakawa a ruwan zafin da kika dora ya tafasa. Sai ki dinga jefawa idan yayi sai ki sauke ki kwashe ki tsane
  • A saka mai da yaji da salad a ci da mai gida da yara
A ci dadi lafiya. Na gode.

Comments