YADDA AKE HADA DAFAFFIYAR DOYA DA MIYAR KWAI

Dafaffiyar Doya da miyar Kwai

Abubuwan hadawa

  • Doya (gwargwadon bukata)
  • Kwai 4
  • Albasa 2
  • Maggi 4
  • Attarugu 3
  • Kori
  • Man girki
  • Tafarnuwa 2
  • Gishiri

Yanda akehadawa

  1. Da farko zaki fere doyarki ki wanke ki sa atukunya da dan gishiri
  2. Idan yayi sai ki sauke ki zuba a kwanonki
  3. Ki fasa kwanki ki jajjaga attarugu ki yanka albasarki
  4. Ki sa kaskonki a wuta kisa mai ya danyi zafi sai ki zuba kwai kisa attarugu, da albasa, da maggi, da tafarnuwa, da kori,
  5. Sai ki dinga juyawa kadan-kadan kar kisa wuta sosai
  6. Idaan yayi sai ki sauke ki kawo doyarki ki zuba
Ana yin wannan cima da safe. A ci dadi lafiya.

Comments