YANDA AKE HADA SINASIR

Sinasir
Abubuwan hadawa
  • Shinkafa ta tuwo kofi 2
  • Albasa 2
  • Suga kadan
  • Yeast chokali 2 babba
  • Nono idan kina bukataba
  • Mangyada
  • Gishiri
Yanda ake hadawa
  1. Da farko zaki sami shinkafarki ki wanke ta ki jika ta.
  2. Idan ta kwana sai ki kai inji a markada miki. Kar a markada miki akan wake.
  3. Idan aka kawo sai ki zuba yeast ki bubbuga ta sai ki rufe ki ajiye a waje mai dumi.
  4. Idan ta dan jima sai ki zuba suga da gishiri kadan da nono kadan don yana kara kyau da tashi.
  5. Sai ki yanka albasarki kanana ki zuba a ciki.
  6. Sannan sai ki dauko farantin suya mara kamu ki dora a wuta sai ki dinga zuba manki kuma ki dinga zuba kullun shinkafarki, sai ki sa marfi ki rufe. Ba a juyawa. Idan ya soyu sai ki cire. Haka zaki yi tayi harki gama.
  7. Ana ci da miyar taushe ko dage-dage ko romon ganda.
Na gode

Comments