YANDA AKE HADA JUICES KALA DABAN DABAN

Lemun citta da lemun tsami
Abubuwan hadawa
 
  • Lemun tsami 6
  • Citta 3
  • Suga
  • Abin kanshi (filabo)
Yadda ake hadawa
 Da farko za ki wanke lemunki sai ki yanka ki matse ruwan a roba mai kyau.
Sai ki wanke citta ki goga da abin goga kubewa sai ki sa ruwa.
Sai ki tace da rariya mai laushi ki hada da lemon tsaminki
Sannan ki zuba sugar da abin kamshi ki juyashi sosai .Sai ki sa a jug ki sa kankara ko kisa a firinji.
 A sha dadi lafiya. Na barku lafiya, sai haduwa na gaba in Allah Ya yarda.

Lemun Abarba da Kwakwa 
Abubuwan hadawa
  • Abarba  (madambaciya 1)
  • Kwakwa  (babbah 1)
  • Madara ta ruwa (1)
  • Sukari kadan  (idan kina bukata)
  • Abin kamshi (flavour)mai kamshin abarba da kwakwa
Yadda ake hadawa
  1. Da farko Uwargida  za ki wanke abarbanki kuma ki yanka kanana sannan ki zuba a blenda ki markada
  2. Idan ya markadu sai ki tace ki ajiye a gefe
  3. Ki fasa kwakwarki itama ki yanka kanana ki markada blenda
  4. Idan ya yi sai ki tace akan ruwan abarbar
  5. Sai ki zuba madara da suga (idan da  bukatar suga din) da abin kamshi
  6. Sai ki juya sosai sai kuma ki zuba kankara ko ki sa a furinji tayi sanyi dan tana bukatar sanyi
A sha dadi lafiya. Na gode.
Lemun Abarba da Madara
Abubuwan hadawa
  •  Abarba 1
  •  Madara ta ruwa 2
  •  Sugar
  •  Flavour (na abarba)
 Yanda ake hadawa
  1. Da farko zaki fere abarbanki, ki yanka, ki zuba a blanda ki markada.
  2. Idan yayi sai ki tace a abu mai kyau, ki zuba madara da sugar da flavour, sai ki juya sosai.
  3. A nan sai ki dandana, idan yayi ki sa a firinji yayi sanyi, a sha dadi lafiya.
Na gode, sai mun hadu a abinci na gaba
GINGER OF ORANGE JUICE
Kayan hadi:-
  • •Citta danya
  • •leman zaki
  • •suger 
  • •flavour
YADDA AKE HADAWA
bare bayan citta wanke idan angama sai a markada a blender,tace ajiye gefe daya.matse lemo da juice mider idan angama sai a zuba wannan cittar a ciki zuba kankara da flavour.za’a sha da sanyi.
GUAVA OF GINGER JUICE
Kayan hadi:- 
  • •Citta danya
  • •Gova
  • •Kanunfari
  • •Leman zaki
  • •Suger 
  • •Flavour 
YADDA AKE HADAWA
dafa suger da kanunfari tace ajiye gefe daya.bare bayan citta wanke sai a markada a jiye gefe daya.markada gova sai a tace,zuba gova da citta,leman zaki a kwano juya kara suger da flavour zuba kankara.a sha da sanyi.
MILK SHAKE
Kayan hadi:- 
  • •Oval tine or milo
  • •Flavor
  • •Suger
  • •Madara
YADDA AKE HADAWA
zuba madarar gari a kwano zuba milo ko ovaltine,zuba ruwa sai a kada shi sosai har yayi kumfa,zuba kankara da suger dai dai bakinka.zuba a jug.idan anga ya kwanta sai akara juyashi. 
PINEAPPLE AND YOGURT ICE
Kayan hadi:-
  • •Abarba
  • •Yoghurt
  • •Flavor
  • •Suger
YADDA AKE HADAWA
yanka abarba markada a blender,tace zuba a kwano,zuba yoghurt akai da flavour,suger da kuma kankara,za’a sha da sanyi.
BREAK FAST NOG
Kayan hadi:-
  • •Madara
  • •leman zaki
  • •yoghurt
  • •nutmeg
  • •ayaba 
  • •suger
YADDA AKE HADAWA
Zuba leman zaki,ayaba,madara da yoghurt a cikin blender idan sun markadu sosai juye a jug,za’a sa a frig(Refrigerator) ko a zuba kankara,zuba nutmeg akai idan kanaso.
TAMARIND JUICE
Kayan hadi:-
  • •Tsamiya
  • •Suger
  • •Kanunfari
  • •Citta
  • •leman tsami
YADDA AKE HADAWA
dafa suger da ruwa barshi ya huce.dafa tsamiya da ruwa,kanunfari da citta har misalin minti 30.tace tsamiyar abarshi ya huce yayi sanyi.
matse leman tsami a kuma yanka guda biyu yankan fadi.hada dafaffan suger acikin tsamiya zuba leman tsami da kuma wanda aka yanka a cikin jug.asaka cikin frig(Refrigerator) yayi sanyi sosai kafin sha.zaka zuba ruwa dai dai tsamin da kakeso kafin sha.
ICE TEA
Kayan hadi:-
  • •Ganyan shayi
  • •Suger
  • •Leman tsami
  • •Na’a-na’a 
  • •Kanunfari
YADDA AKE HADAWA
Za’a dafa duka kayan amma banda suger da leman tsami.dafa suger da ruwa.matse leman tsami a kofi ajiye gefe daya.
Tace ganyan shayi da rariya, zuba suger da leman tsami.
Saka cikin frig(Refrigerator) yayi sanyi sosai.
Idan za’a sha saka ganyan na’a-na’a da aka tsinka guda biyar a ciki da leman tsamin da aka yanka akekkewayo a ciki.a kuma dauki slice daya a yanka bakinsa kadan a saka ajikin bakin kofin.
Za’a sha da strew. 
PINACOLADA
Kayan hadi:-
  • •Kwakwa
  • •Abarba ko leman zaki
  • •Suger 
  • •Flavour na abarba
YADDA AKE HADAWA
Za’a goga kwakwa da abun goga kubewa,markada a blender sai a zuba ruwan sanyi a tace da rariya.markada abarba ko [leman zaki] taceta zuba a kwano.dafa suger da ruwa barshi ya huce.
Hada kwakwa da abarba guri daya ko leman zaki zuba suger da flavour juya sosai asa a frig(Refrigerator) yayi sanyi.
wannan leman ana hadashi ne lokacin da za’a sha.idan kuma aka hada aka sa shi a frig(Refrigerator) za’a ga man kwakwar ya taso,ba lalace wa yayi ba sai akara markadawa. 
FRUIT SALAD
Kayan hadi:-
  • •Abarba
  • •Gwanda
  • •Ayaba
  • •Kankana
  • •Leman zaki
  • •Kwakwa
  • •Leman tsami 
  • •Suger
YADDA AKE HADAWA
za’a yanka duk kayan marmarin kanana-kanana(cubes). Za’a bare leman zaki sala-sala sannan acire kwallon a zubar,a tara totuwar leman da ruwan leman a kofi.
Goga kwakwa kanana.
Matse leman tsami a kwano,yanka ayaba kanana-kanana sai a zuba cikin leman tsami (yin haka yana hana ayabar tayi baki).
Dafa suger da ruwa ajiye gefe daya.
Za’a hada duka yankakkun kayan marmarin waje daya acikin abun da ake hada fruit salad.zuba suger aciki juya sosai.
Idan za’a sha zaka iya zuba condensed milk akan fruits din.
FRUIT DRINK
Za’ayi amfani da duka kayan marmarin da muka yi amfani da su a sama.
Za’a zuba a cikin blender a markada su.
Tace da rariya mai laushi (kara ruwa idan kina bukata).
Zuba suger yadda kakeso ( Idan kina da bukata zuba masa madara).

KUNUN AYA
KAYAN HADI.
  • 1.Ayah rabin kwano
  • 2.Coconut Kwallo biyu
  • 3. Ginger guda
  • 4 kanana 4.Dabino guda 10
  • 5.Swit Potato guda 1
  • 6. Flavor inkina so.
  • 7.Sugar
  • 8.Kankara
YADDA AKE YI
Da farko dai xaki gyara ayanki ki tabbatar kin tsince tsakuwa sai ki sirfa koh kuma inkinaso kijika,in kin sirfa sai ki wanke ayan tass sai ki yanyanka coconut din shikuma dabino ki cire kwallon ciki sai ki kankare ginger kuma kiyanka sweet potato dinki kiyanka kanana duk dai ki dauraye abubuwan da nai bayani inkikagama sai kasa duka acikin ayan ki kara daurayewa sai kisa ishashshen ruwa sai ki nika in annika yai lukwi sai kitace inkikagama sai kisa sugar 2 ur taste sai ki flavor da kankara da ganan asha.
Zobo cikin sauki 
Abubuwan hadawa
  • Zobo
  • Abarba  (rabi - 1/2)
  • Cittah danya
  • Kanunfari
  • Kukumba
  • Sukari
  • Abin kamshi (flavour)
Yadda ake hadawa
Da farko sai ki sa zobonki a tukunya da ruwa, kuma ki sa kanunfari da cittah
Sai ki fere abarbanki da kukumba, ki yanka kanana, sai ki zuba a bilenda ki markada,  sai ki gurza cittah
Sannan sai ki tace da zobonki, kisa sugarki da abin kamshi ki juya sosai, saiki dandana kiji in komai yayi daidai.
Sai ki saka kankara ko kuwa ki sanya firinji don ya yi sanyi, A sha dadi lafiya.
JAMAICAN GUINNESS PUNCH
INGREDIENTS:
1. Malta/Maltina
2. Madaran ruwa biyu
3. Condensed milk
4.Vanilla flavour
5. Pinch of cinnamon
PROCEDURE: Farko dai zaki samu glass cup ko plastic ko rubber, kada kiyi amfani da cokalin qarfe ko kofin qarfe.
Ki juye malta dinki a cup sai ki zuba madaran ki guda biyu, sai ki zuba isashen condensed milk aqalla wanda zai kai girman gwangwanin madaran ruwa, sai ki zuba vanilla flavour tare cinnamon dan dai-dai.
Daga nan sai ki juya sosai su hade, a ido ma zaki ga yayi kauri kadan, in kina da qanqara zaki iya zubawa, in baki dashi kuma ki saka a fridge ya yi sanyi.
Habawa dadi... Yiwa mai house ki ga canji a fuskar sa.
Wannan drink din idan har yaji kayan hadin da na lissafa to ba zaki taba dauka ma malta kike sha ba, saboda ko taste din shi ma ba zai fito ba, amma in kina sha kina jin dandanon malta din to bai ji kaya ba gaskiya. Sannan zaki iya yin sa zallah ba cinnamon ko vanilla flavour kuma still zaki ji mutuqar dadin sa.
ZOBO WITH PINEAPPLE DRINK
INGREDIENTS: 
  • 1.Ganyen Zobo Rabin loka
  • 2.Bawon abarba na abarba daya
  • 3.Flavor na abarba 
  • 4.Sugar 
  • Busashshen Inibi (Grapes) in babu kuma a yi shi haka.
  • 5.Bawon lemu
  • 6.Citta, Kanunfari. masoro, nutmeg da sauran kayan kamshi.
PROCEDURE: Ki sami ganyen zobo ki zuba a tukunya, ki dauraye abarban da kyau, sai ki cire bawon ki zuba a cikin zobon, ki sami busashshen inibi ki sa a ciki, kisa citta, Kanunfari, masoro, nutmeg da bawon ki su dahu tare.
Yana fara tausa za ki ji 'kamshi ya cika gidan, idan ya tausa sosai, sai ki sauke ki barshi ya huce, sai ki tace su, amma ka da ya yi tsululu, sai ki sa flavour da sugar, ki sa a Fridge ya yi sanyi.
Hmm! Zobo fa ba Drink din yara bane, na manya ne, mutanen mu ne ba sa mai kyakkyawar hadi shiyasa sai kahadiye da kyar, amma zobo yana da dadi sosai.
Kuma yana sanyaya zuciyar mai House. Nasan wasu za su ce ni ba zan sa bawo ba, ainihin abarban zansa, maganar gaskiya lokacin da na koya akace 'bawo ni ainihin abarban na sa, amma sai na ji baya qamshi sosai, kuma bayyi mun yadda nayi tsammani ba, da na sake yi na sa zallan bawon sai na ga banbanci. Inibin bushshshe ake sawa, idan baki samu ba sai ki sa bawon abarban kawai tun da yana dadan wuyan samu. Sai an gwada akan san na kwarai.
Sannan akwai foster clerk akwai iri iri a kasuwa, har da mai water melon, zaki ji ya baki kamshi mai dadi.

Comments