Yadda ake Donut
Abubuwan hadawa
Abubuwan hadawa
- Falawa kopi 3
- Bota 1
- Kwai 3
- Mangyada
- Suga rabin kofi
- Gishiri rabin cokali
- Yeast cokali daya
- Baking hoda cokali 1
Yanda ake hadawa
- Da farko zaki tankade fulawarki a kwano mai fadi.
- Sai ki sa yeast da baking hoda ki juya, sai ki sa bota ki yi ta juyawa ya hadu da fulawan sosai.
- Sai ki fasa kwanki ki zuba ki juya ya hadu da fulawan.
- Sannan sai ki zuba suganki a ruwan dumi ki juya sai ki zuba a fulawar ki kwaba da dan gishiri.
- Idan yayi sai ki rufe ki sa a rana yayi kamar minti arba'in.
- Sai ki duba idan ya tashi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada.
- Sai kuma ki kawo gwangwanin madara na ruwa don ki samu yayi rawun sai ki sa a paranti ki dinga murzawa kina sa wannan gwangwanin kina fitar da rawun din donut dinki, kuma ki na sawa a mai kina soyawa, hakan zaki yi tayi harki gama.
Na gode.
DOUGHNUT
INGREDIENTS:
1. Flour Loka, kwano, mudu biyu
2. Butter Simas 1
3. Sugar gwangwani 5
4.Yeast ko wane loka tea spoon cokali biyu idan na qulli ne na 20 naira
5. Egg 8
6. Baking powder two table spoon
8. Flavor cokali biyu table spoon.

PROCEDURE: Farko zaki juye tankadadden flour a roban kwabi, sai ki bude tsakiya ki zuba duka ingredients din, sugar, butter, eggs, da sauran. Wasu kuma su kan zuba yeast a cikin ruwan dumi sannan su zuba.
Daga nan sai ki murje su hade, sai a dauko ruwan dumi ki kwaba dashi. Sai ki buga shi iyakacin bugu, that's in baki da Mixer, ko kuma ki kai gidan bredi su niqa miki shi a injin bredi, zaki ga ya yayi masifar taushi, kawai sai ki sanya shi a rana ya tashi.
Zaki ga ya ciko roba dam, sai ki fara yankawa, sannan idan zaki rinqa diba ki barshi a rufe ne in kika bude zai sha iska.
Sannan idan kin tashi yankawa ko dai ki rinqa yankawa da wuqa ta gefe, ko kuma ki rinqa gutsira ta gefe, ba a cakumosa anyhow zai kwanta miki.
Sannan shi ba a cika masa butter, in kin gadama zaki iya saka oil ludayi daya. Butter yana hana shi tashi ko ya zuke miki mai.
Yawan bugun da zaki masa yayi taushi yawan tashin da zai miki da yanda cikin sa zai kasance. Kuma ki yi kokarin kwaba shi yayi taushi sosai.

Comments
Post a Comment