YADDA AKE HADA LEMIN KARAS

Lemon Karas
Abubuwan hadawa
  • Karas
  • Cittah
  • Sugar
  • Flavour
Yanda ake hadawa
  1. Da farko zaki wanke karas dinki ya wanku sosai sai ki yanka kanana ki zuba a bilenda.
  2. Sai ki wanke cittah itama kiyanka kanana ki zuba a bilenda kisa ruwa ki markada da karas dinki, yayi laushi.
  3. Sannan sai ki tace kisa sugar da flavour. Ki juya sosai sai ki sa a firinji yayi sanyi.
Shi karas yanada kyau sosai wajen kara lafiyar ido.

Comments