YADDA AKE HADA ALKUBUS

KAYAN HADI:-

  • Alkama
  • Fulawa
  • Yis
  • Gishiri
  • Mai
  • Sikar

Yadda ake sarrafawa
1. Da farko za a tankade garin alkama da na fulawa a hade su waje guda, sai a zuba yis da sikari da gishiri a kwaba, amma yafi na fanke tauri.
2. A rufe a kai shi rana, idan ya tashi sai a zuba mai kadan a kara buga shi.
3. Sai a dauko gwamgwani a na shafa masa mai ana zubawa a ciki, ko kuma kukkula a leda kamar Alala.
4. Sai a turara shi. Ana ci da miyoyi irin daban daban

Comments